***
-KADUNA PRESS.
***
Hotuna da bidiyo da suka karade shafukan sada zumunta a ranar Alhamis sun nuna mutum-mutumin kwafin Statue of Liberty na Amurka wanda aka kafa a birnin Jeddah na Saudiyya, abin da ya jawo martani daga hukumomi.

Mutum-mutumin ya bayyana ne a kan babbar hanyar gefen ruwa ta birnin Jeddah, kuma nan take mutane suka fara tambayar hikimar kafa shi.

A wani bayani da hukumomin birnin suka wallafa wanda kuma jaridar Gulf News ta ruwaito, ya bayyana cewa an kafa shi ne na dan wani lokaci domin kawata idon masu yawon bude ido da kayan tarihin Amurka.

Sauyi takwas da Yariman Saudiyya ya kawo a bangaren nishadi
Ranar 4 ga watan Yulin kowacce shekara ne Amurkawa ke bikin samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya, kuma saka mutum-mutumin ya dace da wannan rana.

"Mutum-mutumin Statue of Liberty da aka kafa a kan hanyar Al Hamra wani bangare ne na biki kuma za a cire shi da zarar an kammala," in ji Mohammed al-Baqmi na hukumar Jeddah da kewaye.
Ita kuwa kafar yada labarai ta Al Roeya ta ce wasu majiyoyi sun tabbatar mata da cewa za a yi amfani da Statue of Liberty din ne na tsawon mako daya.

Hakan ya biyo bayan irin wannan yunkuri ne da aka yi na saka wasu abubuwan tarihi na sauran kasashen duniya duka dai domin jan hankalin masu ziyara a birnin.

Ana kallon Saudiyya a matsayin wata jagora ta addinin musulunci, shi ya sa a duk lokacin da ta bullo da wani abu da ba a saba gani ba yake darsa shakku a zukatan wasu da kuma jawo ce-ce-ku-ce.
Wannan sassauci kan harkokin nishadantarwa na baya-bayan nan da Saudiyya ke yi wani bangare ne na shirin da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman yake yi na fadada harkokin tattalin arzikin kasar.
-J.S.A
©Kaduna Press.
-06072019.