Kamar kullum, jima ma da yammacin ranar Asabar6/7/2019 daruruwan yan uwa Musulmi sun fito Muzaharar Kira a saki Shaikh Ibraheem Zakzaky a cikin garin Kaduna.

Yan uwan suna kira ga gwamnatin Buhari kan ta saki Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky wanda take tsare da shi kimanin shekaru uku da rabi ba bisa ka'ida ba.

Shaikh Zakzaky wanda tun a shekarar 2016 wata kotu a Abuja ta yi umarni gwamnati ta sake shi amma bata bi ba, yana fama da matsanancin rashin lafiya sakamakon tasiri da dafin guban harsasan da sojojin Nijeriyal suka harbe shi da su a ranar 13-14/12/2015, yayin da suka kai hari a gidansa suka kashe fiye da mutum 1,000 daga almajiransa ciki har da yayansa guda uku.

#FreeZakZaky
Muhammad Rabeel kaduna
Kaduna Press