Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

ANGUDANAR DA GANGAMI TARE DA MUZAHARA NA WUNI GUDA A BIRNIN LAGOS.


A yau Alhamis 11-7-2019 yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Zakzaky (H) na kudu maso yammacin Nigeria, suka gudanar da gangami tare da Muzahara wanda sukai wuni guda suna gudanarwa a cikin kwarya kwaryar Birnin Lagos.

Wannan gangami da almajiran Shaikh Zakzaky (H) suka gudanar ya samu halartar yan Jaridu daban daban, tare da yan kungiyar rajin kare hakkin Dan Adam, sannan kuma an raba ma al'ummar garin na Lagos takardun makasudin wannan fitowa da yan uwa din sukayi.

Hakazalika kuma alokacin gudanar da Muzaharar yan uwa sun haska Birnin na Lagos da  rubuce-rubucen Free Zakzaky,  da sauran su.

Kuma Alhamdulillah sako ya isa sosai ga al'ummar garin na Lagos mai tarin al'umma.

Daga karshe a ka garzaya Ofishin hukumar kare Hakkin 'Dan Adam ta kasa dake Birnin na Lagos, an kai musu takarda kuma anyi musu bayani game da halin da jagora ke ciki, da take hakkin sa da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke yi. Kuma lallai sunyi ma yan uwa kyakkyawan tarba tare da yin bayani mai ma'ana ga yan uwa.

Ya Allah ka tausaya mana ka faranta rayukan muminai da fitowar Allama Sayyid Zakzaky (H), alfarman Ahlul-Bayt (AS).

Post a Comment

0 Comments

Close Menu