A safiyar yau juma'a 12/7/2019 da misalin karfe 8:00am, a ka gudanar da Jana'iza ta Shaheed Abubakar Aliyu da ke badiko kaduna, shidai wannan shahidi yaro ne dan kimanin shekara sha uku (13) da haihuwa, ya yi shada ne sakamakon harin ta'addancin yan sandan najeriya, da suka kai a kan masu muzaharan lumana ta free Zakzaky a jiya Alhamis 11-7-2019.

Anyi Jana'izar ne a nan garin na badiko a cikin garin Kaduna, Jana'izar dai ya samu halartar Wakilin Musssatu Shuhada Na kasa Malam Abdulhamid Bello, da Wakilin yan'uwa na Kadina Malam Aliyu Tirmiz, da Wakilin Musssatu Shuhada Na Kaduna garin kaduna Malam Aminu U/Rimi da sauran yan uwa da daga janibobin da ban-da-ban. An bizne shi a makabartan da ke tsananin badiko da U/sunusi a nan cikin garin Kaduna.

Muna rokon Allah a amshi shahadar sa ya baiwar iyalansa hakurin wannan rashi. Ya kuma Kwato Mana jagoran mu daga hannun azzalumai.