Jagoran lauyoyin su Malam, Femi Falana ya mike, ya bayyana cewa kotu ta dawo ne yau don ci gaba da bukatar da wanda suke karewa ya gabatar na barinsa ya fita waje don neman magani. Ya ce dukkan sun gabatar da takardu tare da medical report kan wannan. Sannan sun ba da amsa kan abin fa lauyoyin gwamnati suka gabatar. Ya ce yana rokon kotu da ta amince da wannan bukata saboda wadanda ake kara suna fuskantar hatsarin mutuwa saboda raunukan da ke jikinsu. Ya ce ko su kansu lauyoyin gwamanati a takardar da suka rubuta ba su kalubalanci rashin lafiyar wadanda ake kara ba.

Falana ya ci gaba da cewa cikin likitocin da suka yi wannan aiki, akwai likitoci daga qasashen waje tare da taimakon likitoci yan Nijeriya. Yace Bayero Dari, bai kalubalanci dukkan abin da aka gabatar ba. Ya ce Dari ya ce rashin lafiyar wadanda ake kara ba ta da wani  hatsari kuma za a iya maganceta a Nijeriya. Falana ya bayyana cewa dukkan fadin Nijeriya ba wani asibiti da zai iya magance halin da suke ciki nw rashin lafiya. Ya ce ya kuma taba neman DSS da su bar su Malam su fita nemwn magani a qasar waje kan halin da daya idon su Malam ke ciki. Ye ce ammabba su amince ba har idon ya mutu, kuma daya idon yanzu haka yana fuskantar barazanar makancewa gaba daya. Ya ce babu dalilin da Bayero Dari zai kawo na cewa za a iya magance wannan matsala a Nijeriya. Ya ce idan kuma akwai to a ina ne?
Ya ce yanzu haka akwai harsasai a jikin wanda ake kara na biyu. Ya ce zuciyarta kuma na cikin hatsari kamar yadda sakamakon bincike ya nuna. Ya ce daga cikin takardun da suka gabatar akwai takardar bincike da Dr Ramatu ta asibitin koyarwa na Barau Dikko ta gabatar kan wanda ake kara na biyu (Malama Zeenat) cewa tana fada da hawan jini kuma gabobin ta ba sa aiki. Don haka akwai bukatar sai an cire mata harsasan da ke jikinta sannan kuma dole sai an canza mata knee gaba daya. Ya ce duk Nijeriya ba asibitin da zai iya yin wannan aiki.

Bisa dukkan alamu yau Falana ya dauki zafi. Ya ci gaba da cewa dole ne a kula da lafiyar wanda ake kara ko da ya yi laifi, ballantana su da har yanzu zarginsu ake yi. Ya ce dole a kaisu asibiti a New Delhi India manyan likitoci su dubasu, ba wai a Nijeriya ba in da bamu da kayan aiki.

Ya ci gaba da cewa cikin takardun da suka gabatar akwai wadanda asibitin koyarwa na Barau Dikko, aeibitin gwamnati, ne ya yi wannan bincike. Yw ce idan ba a karbi binciken asibitin gwamnati ba a matsayin hujja to na wa za a karba? Ya ce Dr Ramatu Abubakar tana daga cikin wanda suka bayyana cewa ba wani asibiti a Nijeriya da zai iya magance halin da suke ciki. Ya ce Farfesa Bwala ma ya bayyana irin wannan a nashi rahoton da muka gabatar a gaban kotu.

Falana ya ci gaba da cewa binciken ya nuna cewa wadanda ake kara din ana ciyar da su abincin da ke dauke guba. Ya ce wannan kuma DSS ne kawai za su fadi dalilin da ya sa suke ciyar da su da abinci mai guba.Falana ya ce dole kotu da fitar da wadanda ake kara daga hannun DSS da suke ciyar da su guba tun kafin su hallakasu. Ya ce Farfesa Bwala a ranar 10 ga watan July ya bayyana a cikin rahotonsa, hakoran wadanda ake kara  suna komawa bakake, saboda tsananin gudar da ke jikinsu. Sannan wannan abin ne ke kawo wa wanda ake kara shanyewar bangaren jiki. Ya ce wannan hali da wadanda ake kara suna iya rasa rayuwarsu a kowane lokaci.

Falana ya kawo kes din Gani vs Abacha lokacin da aka tsare shi a Bauchi. Shi kuma Falana ya ce lokacin ana tsare da shi a Jigawa, ya ce a mulkin soja ma lokacin kotu ta ba da umarnin dole a bar likitocinsa su rinka dubashi lokacin da suke so. Ya bayyana sunan wani mutum da ake tsare da shi a gidan Yarin Ikoyi, ya ce sun nemi beli amma kotu ta hana. Amma lokacin da ya nemi a barshi ya ce asibiti saboda bashi da lafiya, kotu ta bari an fitar da shi zuwa India, amma an makara domin ya rasu. Ya nemi kotu da ta amince a fitar da su asibiti tun kafin lokaci ya kure. Ya ce mutuwar Malam a hannun jami'an tsaro za ta sama masifa da bala'i ga Nijeriya.

Falana ya ci gaba cewa Lauyoyin gwamnati ba su bayar da wata hujja ba kan kalubalantar fitar da su Malam waje illa kawai ba sa so. Wai suna so ne a yi musu magani a Nijeriya. Ya ce Farfesa Bwala bai ce akwai wani asibiti a Nijeriya da zai iya magance wadannan cukuka da wadanda ake kara suje fama da su ba. Don haka ya ce ba wata hujja da lauyoyin gwamnati za su kawo da za ta hana fitar da su Malam kasar waje. Ya ce tsoron da suke yi shi ne wanda ake karar kila ba za su dawo Nijeriya ba idan aka barsu suka fita kasar waje. Ya ce wannan tsoron ya san wannan kotun za ta cirewa gwamnati shi ta hanyar sanya wani sharadi dw kotun za ta sanya. Ya ce abin da yake rokon wannan kotu shine ta kalli halin da wadanda ake kara suke ciki ta amince da bukatarsu. Falana ya kammala bayaninsa.

Lauyan gwamnati, Bayero Dari ya bayyana cewa wannan rahoton yasabawa sashe. 174 na dokar criminal law na Nijeriya. Dukkan rahoton da aka gabatar an gidashi ne a kan rahoton da aka gabatar a watan Afrilu wanda kuma Islamic Human Right ce ta yi shi kuma ta zabi asibitin da yltake so a kaisu. Ya ce dukkan wani abu da ya biyo baya na rahoto an yi ne don supporting din wannan da human right ta gabatar. Ya ce hakan kuma ya saba da sashe na 174 na dokar criminal ta Nijeriya.

Ya ce umarnin da kotu ta bayar na akawo likitoci daga waje ya ce idan likitocin ba wata kungiya ta kasar wake ba. Ya ce wadanda ake tsare da su ana tsare da su ne don basu kariya. Falana ya mike ya ce dole lauyan gwamnati ya canza harshe, saboda babbar kotun tarayya ta yi huiunci kan wannan. Bayero ya janye maganar.

Bayero Dari ya tabbatar da cewa gwamnati na jin tsoron cewa idan har aka sake aka bar su Malam suka bar kasar nan ba za su dawo ba. Ya ce a cikin martaninsu sunbfadi hakan a sashe na (N). Ya kara da cewa Dr Ramatu Abubakar likitace a asibitin koyarwa na Barau Dikko kuma a lokaci guda kuma itace Likitan wadanda ake kara. Ya ce hakan ya sa ba za a karbi shaidarta ba. Domin bai kamata ta zama likitan gwamnati ba kuma likitan wadanda ake kara a lokaci guda.

Bayero Dari ya bayyana cewa suna da asibiti manya da kuma kayan aiki a Nijeriya da za su iya kulawa da wadanda ake kara. Don haka ne ma wadanda ake karar suke jin dadin wadannan asibitoci tun shekarar 2015. Ya ce suna da Eye Center, suna da Barau Dikko, sannan sun aki su Malam Legos da kuma babban asibitin kasa da ke Abuja. Don haka ya roki kotu da kara da amince da wannan bukata ta fitar da su Malam waje. Bayero ya kammala jawabinsa ya zauna.

Falana ya bayyana cewa tsarin mulki bqi ce kada lauyan gwamnati ya zama lauyan wani ba. Ya ce ba wata doka da ta hana wani zuwa wata kasa neman magani har da Shugaba Buhari yana zuwq waje neman magani. Ya ce manyan yan Nijeriya da dama da ake tuhuma kotuna na basu damar zuwa waje neman magani saboda babu asibitoci masu kayan aiki a Nijeriya. Ya ce babbar kotun tarayya bayyana idan wannan a sharia Dariye da gwamnagin Nijeriya 2015.LPER page 13498.  Ya ce da akwai asibitoci masu kayan aiki a Nijeriya da babbar kotun tarayya ba ta ba da waccan odar ba. Ya ce Asari Dukubo da Gwamnatin tarayya, nekan beli ne, kuma wannan ba beli ake neman ba. Ana beman zuwa asibiti ne kuma a dawo don ceto ran wadanda ake kara don su iya fuskantar tuhumar da ake musu. Ya ce idan wadandq ake tuhuma suka mutu, wa zai amsa hukumar da ake musu? Ya ce a kokarin da Bayero ke yi na kare bukatarsa ya na so ya karyata likitocinsu na gwamnati. Ya ce Dr Ramatu Abubakar ita ce shugaban sashen Family Medicine na Barau Dikko, ya tambaya cewa ya ya nadata wannan mukamin? Gwamnati ce. Saboda haka shi ba shi da ja kan hakan, amma ba wata hujja da ta hana ta zama likitan wani daban.

Mai shari'a Gideon Kurada ya bayyana cewa ya ji dukkan bayanan bangarori bigu din kuma zai yi adalci a kan wannan abu da ke gabansa. Ya ce ranar litinin mai zuwa alkalai za su tafi hutun shekara kuma idanbya tafi hutu ba zai dawo ba. Saboda haka zai saurari sauran shari'un da ke gabansa don haka a dawo ranar litinin zai yanke hukunci. An tashi zaman yau.