Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

JAMI'AN TSARON NIGERIA SUN BUDE WUTA KAN MASU MUZAHARA A ABUJA


A yau talata 09/07/2019, 'yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzakiy suka sake fitowa a Abuja domin cigaba da fafutikar neman 'yancin Jagoransu Sheikh Zakzakiy kamar yadda suka saba yi a kusan tsawon shekaru biyu kullum babu fashi,
Banda wasu lokutan da suka gabata na afka musu da jami'an tsaron Nigeria kanyi.
Yau ma jami'an tsaron sun afka musu babu zato babu tsammani, ta yadda suka kashe mutum guda har lahira suka raunata gomomi daga cikin su.
Shaikh Zakzakiy yana tsare ne tun bayan lokacin da jami'an tsaron Nigeria suka afka masa a mazaunin sa dake garin Zaria a gyallesu bisa zargin mabiyansa sun tarewa hafsan sojojin kasar hanya, zargin da har yanzu mabiyan nasa ke musantawa,
A kusan fiye da shekara guda data gabata kotun mai shari'a mr. Kolawale dake da mazauni a Abuja ta bayar da umarnin sakin shehin malamin ba bisa ka'ida ba, bisa dogaro da hujjojin da aka gabatar a gabanta, kuma a biya shi diyya shi da mai dakinsa na bata musu lokaci da akayi, sedai a mai-maikon hakan 'yan watanni da suka gabata labari ya baza duniya cewa gwamnatin jihar kaduna ta shigar da shihin Malamin kara a gaban wata kotu a jihar, a halin yanzu kes din yana gaban kotun.
-J.S.A
©Kaduna Prss.
-09072019


Post a Comment

0 Comments

Close Menu