Kamar kullun yau 9/7/2019 yan'uwa Almajiran Sheikh Zakzaky, sun fitowa domin cigaba da yin kira ga gwamnatin mr Buhari da ta gaggauta sakin jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa, wanda da take cigaba da tsarewa tsawon shekaru fiye da uku ba tare da laifin komai ba.

Sheikh Zakzaky na tsare tun bayan harin ta'addancin da gwamnatin Mr Buhari ta yi a 12/12/2015, da kaisan mabiyan sa sama da dubu, ciki har da ‘ya‘yansa uku.

A shekarar 2016 babban Kotun dake Abuja ta wanke shi, tace: baiyi laifin komai ba, asake shi. Gwamnatin taki.

A yanzun kuma Gwamnatin Mr Buhari na yunkurin kisan Sheikh Zakzaky ta hanyar bashi guba, da kuma cigaba da rikeshi,  ba tare da kulawa da lafiyarsa ba.