***
-KADUNA PRESS.
***
A jiya asabar 06/07/2019 ne 'yan uwa musulmi mabiya Sheikh Zakzakiy na garin minna suka gudanar da muzaharar neman ganin an saki Shehin Malamin,
Muzaharar wadda aka gudanar da ita da safiyar yau, anfara ta ne karfe goma na safe (10:00am).

Malam Ibrahim Khalil wakilin 'yan uwa na minna ne ya jagoranci muzaharar, kuma an farota ne daga babban masallacin juma'a na garin minna din aka biyo da ita ta bosso road aka biyo ta prison akarshe aka dawo masallaci aka rufe.
-J.S.A
©Kaduna Press.
-06072019.