Daga Abdulmumin Giwa


Amma lallai mabiya Shi'a da ke neman yarda da amincewan gwamnati tare da murna da far in ciki da waki'ar da Harka Islamiyya karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky ke fiskanta, kuna tafka babban kuskure domin wannan mataki da kuke dauka na nuna cewa ku yan Shia ne da ke tare da gwamnati ba dabara bane kuma ba gata bane ga Shia. Kila ma da shuru kuka yi da ya fi muku.

Duk abubuwan da kuke gani suna faruwa da Harka Islamiyya ba su fi abubuwa guda biyu ba da suke da tushe a abubuwa biyu suma.

Na daya akwai hukuma da ta doru akan matsaya ta azzaluman duniya na fada da duk wani tunani da zai jawowa ikonsu a duniya tarnaki. Wadannan kuwa sune America da Isra'ila da sauran kasashen turai da ke musu amshin shata.

Sa'ilinnan, akwai kuma bangarancin addini wato kirkirarren rikicin Shia da Sunna wanda kafircin duniya ke amfani da Saudiya wurin rurutawa musamman a nan Nigeria inda suka samar da Izala da ke da alaka da gwamnati.

Sun ci nasaran cusa kiyayyane da Shia ta hanyan amfani da kirkirarrun kareraki da kuma wanzar da tunani irin na Wahabiyanci a cikin wannan alumma wanda saboda suna tare da gwamnati ake ganin abinda sukeyi kamar shine kawai Musulunci.

Saboda haka, masu kiyayya daga cikn al'umma na kin Harka ne domin an nuna musu cewa yan Shia ne kuma kafirai ne. Ita kuma hukuma na fakewa da cewa tana kin Harkane domin tana adawa da ikonta a matsayin gwamnati.

Haka kuma ita kuma hukuma tana amfani da kiyayyar da aka cusawa, musamman Wahabiyawa, akan  Shi'a wurin samun nasara da fada da takeyi da Harka.

Matsalarsu da Harka shine matsalar America da Israila da Harka wanda shine, a cewarsu, 'influence' din Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Tunda America da Israila da Saudiya na fada da Iran dole yan amshin shatansu su yi fada da Iran a duk inda suke musamman a Nigeria domin influence din kasar a Africa itama.

To ta yaya kuke ganin al'umman da ke fada da Harka domin tana Shia za ta barku kuyi Shi'anci bayan an gama da Harka in har an iya gamawa da Ita?

Hatta gwamnatinma nan gaba ba za ta aminta da Shia'ancin da kuke tunanin yi ba domin kuna da alaka na akida da yan Harka da gwamnati ke neman ganin bayansu.

Saboda haka gatan da kawai kuke da shi itace Harka ba gwamanti ba.

Kuma ku sani duk yadda kuke tunanin cimma burinku wurin ganin kun wanzu a matsayin yan Shi'a ba tare da Harka ba zai zama hasashe ne kawai ba abu mai yiwuwaba. Domin kuwa a wurin yaki da Harka gwamnati na karban shawara da neman goyon bayan masu fada da adawa da Shi'a a Nigeria da kuma umarni daga azzaluman duniya masu neman cimma burinsu na gamawa da kasar Iran.

Kuma ko sun karbi shawararku, a matsayinku na yan Shi'a ba wai don sun aminta da ku bane, sai don su samu lagon ganin bayanku da ku da Harka gabaki dayane.

Ai kuna ji suke cewa gwamnatin Buhari kada ta rantsar da minista Dan Shi'a duk da ba dan Harka bane, da kuma yadawa da sukeyi cewa kada a dauki duk wani Dan Shi'a aikin gwamnati a jihar Kaduna.

Nan gaba dole gwamnati za ta biyewa masu fada da Shi'a domin tabbatar da ganin bayan Harka kamar yadda ta soma yanzu ko ba komai, ko don hujumi da take fuskanta daga wasu sassa na al'umma musamman Kiristoci da yan kudancin kasannan a baya ga tsammani da azzaluman duniya ke da shi akansu. Sai kuma hujumi da suke yi wanda in ba haka ba ba za su samu nasaran wannan burin nasu na nunawa zaluncin duniya cewa sun ci nasara wurin yaki da 'influence' din Iran ba. 

Saboda haka gatanka a matsayin Dan Shi'a a Nigeria ita ce Harka Islamiyya da kuma Jagoran Harkar, Sheikh Zakzaky in dai har Shi'a za ka yi a wannan kasa.

Kwarai za su iya hulda daku yanzu amma bisa yaudara da cimma burinsu ba wai don suna sonku ba.  Kuma, domin kada su rasa goyon baya daga makiya Shianci, a kowane lokaci za su iya sadaukar daku su juya muku baya. Saboda haka ku daina yaudaran kanku.