***
-KADUNA PRESS.
***
A ranar yau Lahadi ce wa'adin da kasar Iran ta bawa kasashen Turai na daukar matakan kare yarjejeniyar da suka cimma kan shirin nukiliyar kasar, bayan ficewar kasar Amurka ya kawo karshe.

Bisa kudiri mai lamba 26 da 37 na daftarin yarjejeniyar, kasar Iran na da hakkin jingine yin aiki da wani bangare na yarjejeniyar da aka cimawa matukar dai wani bangare daga cikin kasashen suka ki yin aiki da abin da yarjejeniyar ta kunsa.

A matsayin mayar da martani na ficewar kasar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar zaman lafiya na kasar Iran da kuma rashin cika alkawarin da kasashen Turai suka dauka na samar da wani tsari da zai kewaye takunkumin da kasar Amurka ta sake kakabawa Iran bayan kwashe shekara guda, Iran ta sanar da dakatar da yin aiki da wani bangare na yarjejeniyar.

Kasar ta Iran dai ta bawa kasashen Turai wa’adin kwanaki 60 a matsayi wata dama domin kare yarjejeniyar wajen cika alkawarin da suka dauka musamman ma na samar da wani tsari da zai kewaye takunkumin Amurka ta yadda kasar za ta ci gaba da hada-hadar kudadenta a bankuna da kuma sayar da man fetur ba tare da wani cikas ba.
-J.S.A
©Kaduna Press.
-07072019.