Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Yan Sanda A Nigeria Sun Nemi Taimako Domin Kama Yan uwa MusulmiRundunar Jamian Yan sanda a Nigeria Sun Nemi Taimakon Alumma Don Kama Yayan kungiyar yan uwa musulmi da ake kira da IMN da Gwamanati ta haramta.

Rahotanni da kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalo ya nuna cewa yan sanda a Nigeria sun neman taimakon alumma da wajen kama mambobin kungiyar yan uwa Musulmi ya yin da suke zanga zanga sakamakon haramta kungiyar da gwamnatin tarrayar Nigeria ta yi,

It adai gwamnatin Nigeria ta haramta kungiyar yan uwa musulmi ne watoIMN bayan taho mu gama da aka yi a birnin Abuja a lokaci da suke zanga zangar neman gwamnatin ta saki jagoransu sheikh Ibrahim Elzakzaki da gwamntin take tsare da shi shekaru 4 kenan domin ya je kasashen waje neman magani, 

lamarin da ya kai ga kashe mutane 20 tare da jikata wasu da dama da kuma awon gaba da wani adadi mai yawa.

A wati sanarwa da sefeto janar din yan sanda Nigeria Mohammad Adamu ya fitar a lokacin da yake bayani ga wasu jami’an yan sanda ya bukaci su yi muamala damambobinkungiyar yan uwa musulmu da ake kira da IMN a matsayin yan yan taadda domin duk wata zanga-zanga ko gangami da zasu yi ya sabama doka tun da an haramtasu.

Post a Comment

1 Comments

Unknown said…
Ina kira ga mutanen gari da karsu shiga wannan al'amari domin hakan zai iya sasu cikin matsala
Close Menu