A yau ne kotun da ke sauraren shari’ar Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran harkar Musulunci a Najeriya tare da mai dakinsa malama Zinat Ibrahim, ke ci gaba da gudanar da zaman sauraren shari’ar.

A zaman da kotun ta gudanar a makon da ya gabata, ta dage zaman sauraren shari’ar, bayan da alkalin kotun ya ce zai yi nazari kan hujjojin da lauyoyin bangarorin biyu suka gabatar a gaban kotun.

Shugaban tawagar lauyoyi masu kare Sheikh Zakzaky Femi Falana San, ya gabatar da bayaninsa dangane da halin rashin lafiya da Sheikh Zakzaky yake ciki tare da mai dakinsa, da kuma bukatar fitar da su domin yi musu magani.

Yayin da shi kuma a nasa bangaren lauyan gwamnati Dari Bayero ya nuna rashin gamsuwarsa da bayanin da Falana ya gabatar, inda ya nuna shakku kan tsanantar rashin lafiyar Sheikh Zakzaky, tare da nuna babu bukatr sai an fitar da shi daga kasar domin yi masa magani, inda ya ce akwai kwararrun likitoci a Najeriya da za su iya duba lafiyarsa.

Alkalin kotun dai ya ce zai yanke hukunci na karshe bayan yin dubi a kan hujjojin da dukkanin bangarorin biyu suka gabatar.
To amma da ga duk kan alamu a Kwai lauje cikin na di, dan yau gwamnati ta baza jami'an tsaro fiye da yanda a kasaba gani, a ranar shiga kotu, hakama cikin kotu, a matakan Tsaro Sosai Harda Police Comissioner yana Kotun a  yau.

To koma dai me nene dai, mu da Allah muka dogara kuma a gare shi muke ne man tai mako.

Wamakaru makarallah wallahu khairal makirin.