Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

A Yau Ne Babbar Kotun Tarayya Ta 11 Da ke Abuja Tafara Sauraren Karar Da Harka Musulunci Ta Shigar Kan Haramata Ta Da Gwamnatin Tarayya Tayi.Kotun ya cika sosai da 'yan jarida. Saboda a cikinta ne za a yi saurarin  kalubalantar ci gaba da tsare dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC a zaben 2019, Mr Sowore.

Babban lauyan Nijeriya, Mr Femi Falana ne zai jagorancin bangaren harkar musulunci da na Sowore a gaban alkali Mr NE Maha.

Jin kadan bayan kammala wasu tsare tsare alkali ya shigo, Samuel Okala, Alex Ajudu, Stanley Omeruwa, Abubakar Marshal, Haruna Magashi su ke wakiktar harkar musulunci, sai Lauyoyi uku suka zo daga ofishin babban mai gabatar da kara na tarayya (AGF).

Samuel Okala ya roki kotu da ta dan jinkirta zaman domin Femi Falana ya samu ya karaso kotun din. Saboda jirgin da ya hau daga Legas ya dan sami tsaiko. Amma ya sauka a Airport yana hanyar shigowa cikin Abuja.

Alkali ta amince da bukatar da bukatar Samuel. Aka dage zaman zuwa awa 1. Za a dawo don fara shari'ar.

Bayan Femi Falana ya iso kotu, a ka sauraren kammala wata shari'a. Sannan a dawo ta Harkar Musulunci da AGF

An kira kes din Harkar Musulunci vs AGF Taye Akota ne ke wakiktar AGF. Falana ya gabatar da kansa da kuma sauran lauyoyin da ya ke jagiranta. Sannan ya roki afuwar kotu saboda jinkirin da ya samu a hanyar Legas. Sannan ya nemi da a ba su lokaci. Don yin nazari

Falana ya nemi da kotu ta basu ranar 2 ga watan Sept don fara shari'a. Amma lauyan gwamnati ya ce ranar yana kasar waje. Kotu ta amince da ranar 11 ga watan Sept don ci gaba da Shari'ar.

Post a Comment

1 Comments

Unknown said…
Godiya Mai yawa Allah yakara sani da daukaka
Close Menu