Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Angudanar Da Bikin Idil Ghadeer A Dai'rar Kaduna.....


A Yau ne 27 ga watan Zulhajj shekara ta 1440 hajira kamariyya, a kayi bikin tinawa da ranar da Manzon Allah (S) ya nasabta Imam Ali (As) a matsayin Khalifa sa a bayan sa, rana ce da ake kira sa Ghadir khuma ko idin Ghadeer.

Taron ghadeer dai Yan shi’a mabiya bazhabar iyalan gidan manzon Allah a duk fadin duniya suna gudanar da bukukuwa a ranar 18 ga watan zulhajj don tunawa da ranar da manzon Allah (s), tare da umurnin Allah a cikin al-qur’ani mai girma, bayan hajjin ban kwana ya tsaya a wani wuri da ake kira Ghadir Khum ya kuma tara dukkan sahabbansa da suke tare da shi a lokacin ya shaida masu cewa Aliyu dan Abitalib (a) shi ne magajinsa a bayan Rasuwar sa.

To Alhamdu-lillah, yan uwa Almajiran Malam Zakzaky na garin Kaduna, suma sun gudanar da wannan biki dan tinawa da wannan rana mai girma.

Taron dai ya gudana a yau laraba 28/08/2019. Da misalin karfe 03:00pm zuwa 03:00pm Sheikh Aliyu Tirmizy wakilin 'yan uwa almajiran Sayyid Zakzakiy na garin kaduna ne ya jagoranci taron. Sheikh Sidi Jawwad ne ya gabatar da Jawabi a muhallin taron, shehin malamin ya yi bayani sosai game da wasiyar da manzon Allah ya yiwa al' ummar sa, da yadda al'umma suka manta da sakon suka zabi son zuciyar su.
Taron dai ya samu halartar 'yan uwa almajiran Sayyid Zakzakiy maza da mata manya da yara, da sauran al'umma da ga da'irar na kadunan.

Muna taya al-ummar musulmi musamman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (s) murnar zagayowan wannan ranar, Allah ya maimaita mana ya kuma sake maimaita mana amin.
Kaduna Press a madadin da'irar kaduna. 

Post a Comment

0 Comments

Close Menu