Babban lauya mai zaman kansa a Najeriya, Mr. Femi Falana, wanda yake bai wa jagoran ‘yan uwa musulmi Sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaky kariya, ya tabbatar da cewa a yau alhamis za su shigar da kara a gaban kotun koli domin kalubalantar hukuncin gwamnati na bayyana kungiyar a matsayin ta ‘yan ta’adda.

Wannan sanarwar ta fito ne jim kadan bayan da ta Harkar Musulunci a Najeriya, ta sanar da dakatar da yin Zanga-zanga na wani lokaci.

Mai Magana da yawun ‘yan’uwa musulmi Malam Ibrahim Musa ya fada a wata sanarwa da ya yi cewa; Daukar matakin jingine Zanga-zangar yin kira da a saki Sheikh El-Zakzaky da mai dakinsa da kuma sauran wadanda ake tsare da su, ya zo ne a matsayin ba da damar bude wata kafa ta warware batutuwan da su ka taro, da su ka hada da kai kara kotu.

Falana ya ce wasu daga cikin ‘yan kungiyar ta ‘yan’uwa musulmi sun tuntube shi, inda su ka bukace shi da ya shirya kalubalantar hukuncin gwamnatin a kotun koli dake Abuja.