KWAMISHINAN 'YAN SANDA YAYI UMARNIN KAMA 'YAN SHI'A A FADIN KASA...-KADUNA PRESS.

Wata takarda mai dauke da bayanai daga bakin kwamishinan 'yan sandan kasar Nigeria Muhammed Adamu tayi nuni da umarninsa dangane da almajiran Sheikh Zakzakiy.
Adamu ya bayyana cewa duk inda aka ga shuwagabanni da sauran manbobi mabiya Sheikh Zakzakiy din a kamasu a dukkanin fadin kasar ta Nigeria, sannan kuma a rushe dukkanin wasu gine-gine nasu.

Adamun ya bayyana cewa inba'a manta ba a ranar 22/07/2019 ne suka gudanar da wata muzahara wadda ta janyo sanadiyyar rasa ran DCP Umar K. Usman, da precious Owolabi.

Hakanne ya sanya aka samar da kwamitin bincike na musamman akan lamar, wanda kuma yayi nisan gaske a cikin aikin nasa.

Kwamishinan ya nunawa al'umma cewa su aukawa 'yan uwa musulmin a duk inda suka tsince taron nasu.

-J.S.A
©Kaduna Press.
-31082019.