BAN SAN MENE NE ULTERIOR MOTIVE DA ALZAKZAKY YA YI BA.

In ji Sheikh Zakzaky Daga NEW DELHI INDIA.

Bismillahir Rahmanir Raheem, Wasalallahu Ala Sayyedina Wa Nabiyyena Muhammadin Wa Alihi Addayyebinad Daheereenal Ma'asumeen.

Wani abin da zan qara bayani dangane da abin da na fada dazu shi ne, mun yi magana da shi wani jami'in jakadancin Nijeriya a nan, a kan yana cewa akwai mafita? Akwai wani abu wanda ba mu so ne, wanda muka gani a nan sai su yi magana a kawar. Na san kuma mai yiwuwa yana maganar 'yan sandan da aka zo aka sa a qofar dakinmu ne. 

To sai ce masa, to, eh ina ganin qila dai wannan asibiti ba zai yiwu ba saboda lallai siqqa dinmu da wannan asibiti ya kawo qarshe, tunda dama an bamu shawarar wannan asibitin ne a kan cewa, su likitocin da suka je Nijeriya su suka bamu wannan shawaran. To, amma kuma yanzu da muka zo sai muka ga cewa wani abu muka gani gaba daya, an ce mana wadannan likitocin ma ba za su iya, ba ma da su za a yi aiki ba, sai dai kawai suna iya ba da shawara.

To, shi ke nan sai muka ga komai dai, ba sai na maimaita maku abin da na farfada ba, siqqa din mu dai da wadannan mutanen na ce ya riga ya qare, saboda haka yanzu muna neman, sai yace to akwai wani mafita? Sai na ce mafita ana iya in aka ba mu dama mu tattauna da su wadannan likitocin da muka sani da kuma wasu 'yan uwanmu da muka sani wanda suke zaune a nan. Na ce cikin likitocin ma akwai daya ya taso daga London zai iso nan a jiya ke nan, zai taso ya iso. Sannan sauran daya daga cikinsu ya je Hajji mai yiwuwa bazai dawo ba har mu gama tattaunawa, amma kuma suna iya kawo mana wadanda suma suka aminta a tattauna, in akwai wani asibiti da su kuma suka amince, suka bamu shawarar a je can to, za mu yarda a koma can.

Wannan ke nan, in kuma har bai yiwu ba ne, sai ya ce to. In kuma har an aminta da wannan tattaunawar ba lallai za mu zauna a nan asibitin ne kamar gidan yari ba, sai a kai mu wani hotel, fasfunanmu (Passports) na hannunsu ne. Sannan sai mu tafi tare da wadanda suka rako mu, ko kuma mai'aikatansu da suke nan, su zauna suna gadinmu a qofar. Su kuma 'yan sanda ba mu qi ba, in ma za su yi gadin ne sai su yi a wajen hotel din ba a cikin hotel ko a qofar daki ba, har mu warware wannan. In mun warware wannan to, shi ke nan.

To sai ya ce, to  tunda shi kamar dan saqo ne zai je ya gaya ma na gaba da shi, zai kuma dawo mu ji me  ya faru. To wannan daga cikin abin da nake so in warware.
Sannan kuma cewan da suka yi wai  an fara wani Ulterior Motive tun a Dubai, mene mene? Wannan dai to, kun san dai irin magana irin tasu. Muna Dubai mu dai mun tattauna da shi daya daga cikin wadannan aka yi introduction  wannan shi ne wane, wannan shi ne wane cikin muna raha. Tunda ya ce ba mu sami yi a Abuja ba, haka nan muka taso ba sanayya. To, muka sassan sunayen juna.

Sannan a ciki ne sai nake ce masa to, ka ga na ga ku kuke riqe da fasfunanmu (Passports) kuma komai na hannunku, amma in muka je Delhi muka sauka, to, lallai ni ba zan yarda in bar filin jirgin sama ba, sai na ga likitocin da muka amince.
To, ko da muka zo kuma sai muka samu wasu likitoci suka ce su ne ainihin likitocin wannan asibitin da za mu je. Suka gabatar da kansu. Sai muka tafi, har muka masu ma ai duk mu family ne mu goma sha daya. Wato, da mu biyar da su 'yan rakiyar gwamnati guda shidda. Haka nan sai na ce masu mu family ne guda goma sha daya, kuma haka aka karbe mana fasfunanmu mu goma sha daya. Har ma aka qidaya aka tabbatar mu goma sha daya ne, aka wuce da mu immigration, sannan kuma aka biyo aka karbi kayanmu duk aka loda a wuri guda.

Sannan aka ce mu za mu shiga ambulance  ne, sauran kuma za a zo da su a wasu motoci, kuma hakan aka yi. Aka kawo su har kayansu ma har nan asibitin, sannan aka kwashe aka kai hotel din da suka sauka. Har ma wasu kayanmu suka je can hotel dinsu; wasu kayansu kuma aka bar su a nan. Haka nan har mukai musanyan kaya. Ni ban ga wani abu da za a kira shi ULTERIOR MOTIVE a wannan abin ba. Sannan fasfunanmu duk guda goma sha dayan aka damqa masu a hannunsu. To, ban san mene ne ULTERIOR MOTIVE da al zakzaky ya yi ba?

Sannan da muka zo nan kuma bayanan da muka yi maku, yadda su suka dauke  mu a matsayin an kawo marasa lafiyan da basu san ma ciwon da suke yi ba. Alhali mu mun fito ne saboda wa'yansu cututtukan da muka sani, wanda suka gagari magani a gida a kan shi ne muka zo. Ba mun zo ne a ce wai tun farko ma ba a san me ke damunmu ba, za a bincika ba. Shi ya sa kuma ba mu yadda da wannan cewa tun farko za a bincike mu ne. Mun yi tunanim abin da ya kawo mu ne ake nema a canza. To shi ne wannan bayanan ke nan da suke cewa  wai an qi bin qa'idoji.
Sannan kuma mun fahimci cewa, mu suna gaya mana ku ne kuka za6i wannan asibiti, ku ne kuka kawo kanku, don mu mmukakawo kanmu ba su sukakawo mu ba. Amma su abin da suke ce ma jami'an gwamnati na nan Indiya sune suka kawo marasa lafiya, saboda haka gwamnatin Indiya tana taimaka masu a kan su kaimu a tsare wa'yannan marasa lafiya wanda suka keto ma da miyagun laifuffuka. To, wannan sura da suka bayar shi ya dagula, ya canza surar gaba daya. Alhali a surar da yake, mu me muka za6i muje wani asibiti, muka ayyana sunansa, aka ce kuma jami'an gwamnati su sa ido.

To yanzu sai muka ga ba ido kawai suka sa ba, sun sa baki, sun sa hannu, kai har qafa ma sun sa sun ham6are. Duk sun lalata komai ya zama su ba sa ido sukai ba, sun ce ma sune komai da komai. Wannan kuma ba yadda za ai bayan sun wannan su zo su ce za su murguda bayani su zo su ce wai mu ne da laifi, alhali sun san abin da suka aikata. Wannan dai dan qarin bayani ne.
Wassalamu Alaikim Warahmatullahi Ta'ala Wa Barakatuhu.
150419