Harka Islamiya a tarayyar Najeriya ta shigar da kara a gaban wata babbar kotu a Abuja babban birnin kasar inda take kalubalantar haramtata, wanda gwamnatin tarayyar ta yi a makon da ya gabata.

Lawyoyin Harkar Musulunci sun bayyana cewa haramcin ya sabawa kundin tsarinmulkin kasar don haka sun bukaci babbar kotun ta shiga tsakani don maido masu hakkinsu.

Kafin haka dai a makon da ya gabata ne gwamnatin tarayyar ta sami izinin wata babban kotu a Abuja na haramtata Harka Ismiyya da kuma maida ita a matsayin kungiyar 'yan ta’adda, kamar yadda gwamnatin ta bukata daga kotun.

Magoya bayan harka Islamiyya karkashin jagorancin sheikh Ibrahim El-zakzaky dai sun dau lokaci suna fitowa kan titunan birnin Abuja domin neman sakin jagoransu wanda gwamnati take tsare da shi tun a karshen shekara ta 2015.