A jiya Lahadi hukumar tsaro ta farin kaya wato SSS ta kira taron manema labarai a birnin Abuja, inda ta bayyana dalilinta na kama Omoyele Sowore, mai kamfanin jaridar Sahara Reporters ta intanet kan shelar da ya yi ta Revolution Now da ke nufin juyin juya-hali.

Mai magana da yawun hukumar tsaron ta farin kaya, Peter Afunanya, ya ce suna da cikakkiyar masaniya kan goyon bayan da Mista Sowore yake samu daga kasashen waje da nufin tayar da tarzoma a Najeriya ta hanyar shelar da ya yi ta samar da sauyi a kasar'.

Sai dai jami'in hukumar bai fadi ko yaushe ne za a gurfanar da mista Sowore a gaban kotu ba.

A bangare guda kuma fitaccen marubucin nan wanda ya taba lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya yi tir da tsare jagoran masu fafutikar kare hakkin dan Adam, inda ya nemi jama'a su nuna rashin amincewa da sha'anin kasar nan.

Mista Sowore wanda ya yi takarar shugabancin Najeriya a yayin zaben kasa na 2019 karkashin jam'iyyar AAC, ya shiga hannun hukumar jami'an tsaro na farin kaya a ranar Asabar biyo bayan kiran da ya yi na neman jama'a su nuna rashin amincewa dangane da yadda al'amura suka tabarbare a kasar.

A sanadiyar wannan kamu da aka yiwa Sowore, Farfesa Soyinka ya misalta lamarin da rashin adalci da kuma dakile 'yancin dan Adam wanda kundin tsarin mulkin kasa ya yi tanadi.