Wannan aikin Allah ne, ba aikinmu bane, mu guji cika baki, mu guji mummunan magana, mu manta da abubuwan da mutanen gari suka yi mana, mu basu uzuri, sun jahilcemu ne, idan suka fahimci abin da muke yi zasu zo ayi dasu.

Kada wani dan uwa ya ga aikinsa shine yafi bada gudumuwa, Mu guji tsokana da maganganu marassa kima. Mu kara dogaro ga Allah, Mu yi fatan Allah ya ringa dauramu akan Azzaluman da ke Zaluntarmu.

_Shaikh Yaqoub Yahya
Wajen Addu'a yau Litinin

5 Aug2019.