Kaduna Press
Daga Ukhasha Ibrahim, Mukhtar Ahmad

Idan Aka Gama Da Elzakzaky, Kaine Target!!!

Sheikh Abubakar Kamaluddeen, Jagoran Shi'a a Ghana Kuma babban Malami dayake da Dalibai a duk sassan Kasashen Yammacin Africa, Ciki kuwa Harda Nigeria,Kamar Sheikh Abu Jaja,Sheikh Abbas Sha'aban Daga Ghana, Sheikh Jabaati daga Mali,Sheikh Azeez Mustafa daga Benin, Sheikh A/razak Togo  Sai Kuma uwa uba Sheikh Bashir Auwal da Saleh Zaria Wadanda Suna Cikin Jiga-jigan Qungiyarnan Ta (RAAF) a Nigeria.

Shehin Malamin Yayi wannan Furuci ne a ranar Lahadi 18-8-2019, a wajen Ghadeer Wanda Ya gudana a Markazu Imam BaQir dake Nima,Accra,Ghana.

A farkon jawabinsa Ya baiyana Sheikh Zakzaky a Matsayin babban Alami a cigaban Shi'anci a Nigeria dama Duniya baki daya, a inda yake cewa"" Sheikh Zakzaky Mutum ne wanda Yake babu Shakka Dan Shi'a ne, Kai!! Ya bari Shi'anci Ya zama ma'arufi(sananne) a duniya ta yanda wadanda ba Musulmi bama Sun Fahimci abinda ake cema shi'anci Saboda Zakzaky.

Ya kuma nuna Takaicinsa game da abinda wasu Almajiransa dake Nigeria Sukeyi na adawa da nuna Hassada ga Sheikh Zakzaky, inda yake cewa'' Tijjanawa da Wahabiyawa(Izala) Ragunan Amerikawa ne ,aduk sanda sukaso zasu Yankasu Su cinye Namansu da Fatunsu gabaki daya, wannan Yasa basa matsa masu, Amma wadanda Suka zama Threat (barazana) sune 'Yan Shi'awa a duk Fadin duniya, Kuma sune target dinsu a koda yaushe.

A Qarshe yayi kira da jankunne Ga wadannan Daliban nasa Na Nigeria akan cewa Matukar Suka goyawa gwamnati baya wajen Murkushe Sheikh Elzakzaky, To Target na gaba zai zama Shine Gwamnati taga bayansu, Inda yake cewa"To inaso ka gane in aka kare da Elzakzaky, Kaine target. Saboda babban target dinsu Shine Shi'anci. Sannan Yayi Kira dangane da Muhimmacin Hadin kai tsakanin 'Yan Shi'a.