Hukumar jami’an tsaron farin kaya ta bada sanarwan cewa tana shirye-shiryen bin umurnin kotu dangane barin sheikh Ibrahim Zakzaky zuwa kasar India don jinya.

Kamfaninin dillancin labaran NAN ya bayyana cewa a jiya litinin ce wata babban kotu a Kaduna ta a amince shugaban Harka Islamiyya a najeriya Sheikh Ibraheem da matarsa malama Zinat don jinya a kasar Indiya tare da wasu sharruda.

Tun shekara ta 2015 ne dai ake tsare da sheikh Zakzaky bayan dirar mikiyan da jami’an tsaro suka yi masa da mabiyansa a gidansa dake unguwar gellesu a birnin Zaria Nageria.

A halin yanzu dai albarusai da raunuka da suke cikin jikinsu ne suka galabaitar da su wanda ya zama tilas a fita da su zuwa kasashen wajen don jinya.

Kakakin hukumar ta DSS Peter Afunanya ya tabbatar da cewa sun karbi umurnin kotun kuma sun fara aiki don aiwatar da shi.