Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

WANI SHIRI GWAMNATIN EL RUFA'I KE YI GAME DA ASHURA A KADUNA?.....Kamar yadda mahukunta dauri basa daukan darasi, haka ma na yanzu basa daukar darasi.

Gwamnatin jahar kaduna karkashin Nasiru El rufa'i har yanzu, basu saduda ba, a kan abin da suka yi wa, Sheikh Zakzaky da Almajiran sa a kaduna da zaria.

Rohani daga majiya mai tushe, ya tabbatar mana da cewa yan Kato da gora su ta Shirye-shiryen Dirarwa Yan'uwa Musulmi. Almajiran Sheikh Zakzaky, a lokotan da suke gabatar muna sabobin Ashura a kaduna.

Labarin da muka samu tun kusan sati daya na nuni da cewa rundunar ‘Yan Kato da gora na jihar kaduna karkashin jagorancin Nasiru El rufa'i, sun yi zama a kan shirin afkawa almajiran Sheikh Zakzaky na kaduna, shugaban yan Kato da gora (civilian j.t.f) alhaji Ali Sokoto ne ya jagoranci zaman a tudun wada kaduna.

A lokacin zaman a cewarsa sun yi zama da gwamna Nasiru El Rufa'i ya shaida masa yan sandan sun kasa biya masa bukata, na dakile almajiran Sheikh Zakzaky, a garin kaduna, dan haka ya amsa wa gwamna su za su iya, amma suna da bukatar kudi dan ai watar da hare-hare a yayin zaman makokin imam Hussain (As) a nan garin kaduna.

Sannan muna da labarin wata mata kirar Hilux da bakin tinted glass, mai number 10A03KD, sun zo Fudiyyah rigasa da yan sanda a farin kaya a mashina mutane takwas (8) a mashin hudu (4), sun zo sun dauki hotunan. Suka koma nan police station na rigasa.

A Sama da shekaru 40 almajiran Sheikh Zakzaky sukan gudanar da tarukansu bisa tsari da nizami ba tare da cuta ko cutarwa ga kowa ba, bugu da kari al'ummar kaduna su shaida cewa almajiran Sheikh Zakzaky mutane ne masu neman zaman lafiya har ga wanda ya zalunce su, la'akari da abubuwan da suka faru a lokutan mulkin gwamnatocin baya da na yanzu.

A saboda haka muna kira  yan Kato da gora civilian j.t.f da al'ummar jahar kaduna dama na tarayyar Najeriya ga baki daya cewa, kwamishinan ‘yan sandan jahar Alhaji Ali Sakkwato da El Rufa'i sun anso kwangilar shirya shekar da jinin almajiran Sheikh Zakzaky a jahar, a jahar kaduna.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu