Kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayya Afrika, ya bukaci da a dama da kungiyar wajen lalubo hanyoyin magance rikicin kasar Libiya, wannan kuwa ta hanyar nada wani wakili na hadin guiwar kungiyar ta AU da kuma MDD kan kasar ta Libiya.

A cikin wata sanarwar bayan taron ministocin kasashen na Afrika da kasar Morocco ta shirya, a daura da taron koli na MDD, kwamitin na AU, ya bayyana matukar damuwarsa akan yadda al’amuran tsaro ke kara dagulewa a kasar ta Libiya.
A cewar kwamitin zaman lafiya da tsaron na Afrika, rikicin na Libiya babbar barazana ne ga yankin dama nahiyar baki daya.

Wannan dai na zuwa ne bayan da a ranar Alhamis data gabata, Janar Khalifa haftar, ya bayyana cewa a shirye ya ke, kan tattaunawa, saidai kuma a nasa bangare shugaban gwamnatin hadin kan kasa dake samun goyan MDD, Fayez al-Sarraj, ya yi watsi da wannan tayin a zauren taron MDD, tare da yin tir da sanyan hannu wasu kasashen ketare a rikicin kasar da a cewarsa suke ingiza abokin hammayarsa tasa.

Ko ranar Alhamis ma kasashen mambobin kwamitin tsaro na MDD, (Amurka, Rasha, Biritaniya, Faransa da kuma China), tare da kasashen Italiya, Hadadiyar Daular Larabawa, Jamus da Turkiyya da kuma Masar, sun gudanar da wani taro a daura da babban taron MDD da nufin sasanta bangarorin dake rikici a kasar ta Libiya, inda wasu ke goyan Haftar wasu kuma Al-Sarraj, saidai a cewar rahotanni babu wata wani bayyani da ya fito kan taron, wanda kuma manuniya ce ta cewa har yanzu akwai sabani tsakanin kasashen kan yadda za’a shawo kan rikicin kasar ta Libiya.