Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Aljeriya : An Gurfanar da wadanda ake zargi da ingiza masu boreWata kotun soji a birnin Blida na Aljeriya, ta fara sauraren wasu mutane da ake zargi da ingiza masu zanga zangar data ki ci taki cinyewa a kasar.

Mutanen da aka gurfanar a jiya Litini, sun hada da wani dan uwan tsohon shugaban kasar mai murabus Abdelaziz Bouteflika, da wasu tsaffn jami’an hukumar leken asiri ta kasar da kuma shugabar wata jam’iyyar siyasa ta adawa.

Ana dai zargin mutanen da manakisa kan gwamnati da kuma zagon kasa wa sojoji.
Bayanai daga kasar sun ce an jibge tarin jami’an tsaro na ‘yan sanda da na Jandarma da kuma sojoji a gewayen kotun.
Rahotanni sun ce an kore duk ‘yan jaridan da suka nufin kotun, a don haka babu wani karin bayyani da aka samu dangane da zaman kotun da za’a ci gaba da gudanarwa a cikin sirri.

Wadanda ake zargin dai zasu iya fuskantar hukuncin dauri gidan yari, da ya kama daga shekaru biyar zuwa goma, har ma zuwa daurin illa ma sha Allahu.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu