Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi, ta sanar da fara gudanar da bincike a hukumance, kan bukatar tsige shugaban kasar Donald Trump, game da tattaunawar da ya yi ta wayar tarho da shugaban Ukraine.

A jawabinta, bayan kammala wani taron sirri da 'yan jam'iyyar Democrats na majalisar, Nancy Pelosi, ta ce tana sanar da yunkurin majalisar na fara bincike kan bukatar tsige shugaban kasar.

Shugabar, ta ce za ta ba kwamitocin majalisar shida umarnin fara bincike kan Trump, kan bukatar ta tsige shi da ‘yan democrat suka bukata..

Saidai da yake maida martani kan yunkurin, shugaba Trump, ya bayyana matakin a matsayin "cin zarafin shugaban kasar", yana mai cewa, matakin na tsige shi, bita da kulli ne.