.Rahotanni sun bayyana cewa yau litinin ce gwamnatin kasar Kamaru ta bude taron kasa a birnin Yawunde babban birnin kasar, domin fara tattaunawa game da batun rikicin masu neman ballewa daga kasar dake arewa masu yammanci da kudu masu yamamcin kasar.

Raboton ya ci gabab da cewa Shugaban kungiyaraware din da aka gayyata ya nuna ba zai halarci zaman ba , sai dai idan za’a gudanar da shi a wajen kasar da kuma kuma sanya mai shiga tsakani daga wajen kasar kuma ba dan kasar Kamaru ba.

Sai dai gwamnatin kasar ta kore wannan bukatar, tare da nuna kin amincewa da sanya mai shiga tsakani daga wajen kasar. 

ta kara da cewa ta gayyaci sama da mutane 1000 da suka hada da yan majlisa, malaman makaranta , kungiyoyin fararen hula da malam addinai, kuma wanna taron ya gudana ne karkashin jaograncin Pira ministan kasar Joseph Dion Ngute .