Rahotanni dake fitowa daga jihar Zamfara sun nuna cewa shirin sulhu da tabbatar da zaman lafiya da gwamnatin jihar ta dauka na ci gabda samun nasara, inda a baya bayan nan aka ceto mutane 372 da aka yi garkuwa dasu , kana an samu bindigogi sama da 240 da masu garkuwa da mutane suka bayar.

Ana shi bangaren kwamishin yan sanda na jihar Zamfara Mal Usman Ungogo wanda ya jagorancin zaman sulhu da sasantawa da aka gudanar agarin bakura ya bayyana cewa da dama daga cikin wadanda ke garkuwar da mutane domin karbar kudin fansa a wasu jihohi ba Fulani ba ne sun kunshi matane da suka fito daga kabilu daban daban na Nigeria.

Har ila yau ya zargi kungiyoyin yan banga da aka fi sani da yan sakai da alhakin kara tabarbarewar tsaro a jihar sakamakon hare haren da suka rike kai wa tare da kashe mutane ba bisa tsari ba, da hakan ya jawo kar hare haren daukar fansa.

Daga karshe ya nuna gamsuwarsa game da irin ci gaban da aka samu daga lokaci kafa kwamitin sulhu da sasantawa