Wasu Mutane da ba a san ko su waye ba sun kai hare-hare kan gidajen jagororin 'yan adawa a kasar Sudan.

Jaridar AlQudus Arabi ta ruwaito jam'iyar Al-Mu'utamar na cewa wasu gungun matasa da ba a kai ga gane ko su waye ba sun kai hari kan gidan Sharif Muhamad Usman shugaban jam'iyar a birnin Khartoum fadar milkin kasar Usman na daga cikin shugabanin gamayar kungiyoyin hadaka na neman sauyi da 'yanci da suka jagoranci gwagwarmayar kifar da gwamnatin hambararen shugaban kasar Umar Al-bashir.

Har ila yau sanarwar ta kara da cewa gungun matasan sun kai irin wannan hari a gidan Muhamad Husain Sayyid shugaban wata kungiyar farar hula da kuma gidan Nihal Umar daya daga cikin shugabanin kungiyar Al-Mu'utamar dukkaninsu jigo ne a gamayar kungiyoyin neman sauyi da 'yanci da suka jagoranci kifar da gwamnatin Al-bashir.

Tuni dai jam'iyar ta Al-mu'utamar ta yi tir da kai harin tare da bayyana da shi da wasan yara, inda ta ce hakan ba zai sanya zuciyarmu ta karaya ba wajen ganin an tabbatar da tafarkin Demokaradiya a kasar ta Sudan.