Rahotanni daga Afganistan na cewa an kai jerin hare hare da dama, yayin da ‘yan kasar ke kada kuri’a a zaben shugabancin kasar na yau Asabar.

Hare haren na daga cikin alwashin da kungiyar Taliban ta tauka na hana gudanar da zabukan data kaurace ma.

Bayanai daga kasar sun ce an kai hare hare a birane da dama na kasar, saidai babu cikaken alkalumma akan irin barna ko hasara da aka samu.

Tunda farko dai an jibge kimanin jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji kimanin 100,000 domin tabbatar da tsaro a zaben wanda ‘yan takara 16 ke fafatawa, ciki har da shugaban kasar mai barin gado.
Kimanin mutane miliyan 10 ne sukayi rejisrta a zaben a hukumance, saidai saboda fargaba akan matsalar ta’addanci, ba’a samu fitowar jama’a sosai ba wajen kada kuri’a.

Wasu rahotanni sun ce mutane kadan-kadan ne suka fita zuwa kada kuri’a, a yayin da motocin ‘yan sanda ke sintiri a manyan tituna, musamman a Kabul babban birnin kasar.