Rahotanni daga Iraki na cewa an kai wasu harin hare hare biyu dab da ofishin jakadancin Amurka dake birnin Bagadaza.
Wani Jami'in tsaron kasar Iraki ya bayyana cewa, an kai harin boma-bomai biyu a wani wurin dake dab da ofishin jakadancin Amurka dake birnin Bagadaza na kasar Iraki, sai dai babu wanda ya ji rauni a sakamakon harin.

Bayan abkuwar harin, an kunna jiniya don yin kashedi ga jama'a a yankin mai cike da zaman lafiya, da kara daukar matakan tabbatar da tsaro.

Mazaunan wurin sun bayyana cewa, sun ji fashewar boma-bomai a cikin yankin zaman lafiya.

Yankin yana tsakiyar birnin Bagadaza, kuma hukumomin gwamnatin kasar Iraki da ofisoshin jakadancin Amurka da na Birtaniya dake kasar suna cikin wannan yanki.