Kafafen watsa labarun kasar Saudiyya sun ambaci cewa an kashe Abdulazizi al-Fagam wanda shi ne mai tsaron sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulaziz na shekaru masu tsawo.

Jaridar al-sharqaul Ausat ta Saudiyya ta ce; abokin mai gadin sarkin na Saudiyya ne ya kashe shi bayan da su ka sami sabani. Sai dai har yanzu babu wata majiyar gwmanati wacce ta tabbatar da dalilin kashe al-Fagam.

Wani mai fafutuka na kasar Saudiyya, Aliyul Ahmad ya fadawa tashar talabijin din ‘al’alam’ cewa; Al-fagam ya mutu ne daga harbinsa da harsashi da aka yi, kuma kwanaki kadan da su ka gabata ne aka sallame shi daga aiki.

Majiyar ‘yan hamayyar siyasar kasar Saudiyya na nuna shakku akan yanayin da ya kai ga kashe mai gadin sarkin na Saudiyya.