Gwamnatin Najeriya ta sanar da katse layukan wayar hannu miliyan 2 da dubu 277 da 311, wadanda ba a yi musu rijista ba, ko kuma cika ka’idoji wajen yi wa layukan rijistar.

Daukar matakin dai ya biyo bayan umarnin da Ministan Sadarwar Najeriya Dr Isa Ali Pantami ya baiwa hukumar lura da harkokin sadarwa ta Najeriya NCC a ranar 12 ga watan Satumba, na katse layukan, har zuwa lokacin da masu su suka cika ka’idojin yin rijista.

A lokacin Ministan ya bada umarnin dai, ma’aikatar lura da harkokin sadarwar Najeriya ta ce layuka wayoyi miliyan 9 da dubu 200 ne basu da rijista, sai dai a yau asabar, ma’aikatar ta ce zuwa 25 ga watan na Satumba da muke ciki, an yiwa miliyan 6 da dubu 830 da 249 rijista, daga cikin miliyan da suka saba ka’ida.