Ministan wurare da cibiyoyi na al’adu da kuma sana’o’in hannu ya bayyana cewa; A cikin shekarar hijira shamshiyya da ta gabata an sami karuwar masu zuwa Iran yawon bude ido da kaso 38%, wanda ya kai adadin mutane miliyan 4.

Ministan kula da wurare da cibiyoyin al’adu, Ali Asgar Munisan ya fada a daren jiya Laraba cewa; Makon yawo bude ido, da kuma ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware akan harkokin yawon bude ido.

wata babbar dama ce ta gabatar da wasu shirye-shiryen akan batun da su ka hada da yadda masu hotel-hotel a gundumar Karman tafiyar da nasu harkokin.
Ministan ya yi ishara da wuraren yawo bude da ake da su a cikin gundumar ta Karman masu kayatarwa.

Iran dai tana da cibiyoyi da wuraren tarihi na dubban shekaru da masu yawon bude ido daga kasashen waje suke kai ziyara domin kashe kwarkwatar ido.