Rahotannin da suke fitowa daga birnin Dar es Salaam na nuni da cewa an sami raguwar kananan yaran da suke gararamba akan tituna bayan da gwamnatin kasar ta fara aiwatar da tsarin karatu kyauta.

Jaridar “ The Citizen’ ta kasar ta Tanzania ta buga rahoton cewa; Tun daga shekarar 2015 da aka kaddamar da shirin na bai wa yara ilimi kyauta,yaran suka shiga makarantun Piramare da Sakandire
Bugu da kari, gwamnatin kasar tana daukar yaran da suke kan tituna tare da mayar da su zuwa ga iyayensu.

Asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef ya bayyana cewa; Da akwai kananan yara da adadinsu ya kai miliyan 30 akan titunan kasashen nahiyar Afirka.