Jami'an tsaro a Najeriya sun sanar da daukan matakan bincike na takardar dan kasa domin tattance masu laifi a jihohi uku na arewa maso gabashin kasar

Cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan lahadi,Rundunar sojin Najeriya ta bukaci ko wani dan kasa ya kasance da katinsa na zama dan kasa a duk inda zai tafi , a wani shiri da suka kaddamar na gudanar da bincike domin gano mayakan boko haram da suka saje a cikin al'umma.

Wannan mataki da Rundunar tsaron Najeriyar ta dauka na zuwa ne bayan wasu bayyanan sirri da ta samu na cewa wasu daga cikin mayakan boko Haram sun saje a cikin al'umma a gariruwa da kauyuka na jihohin uku na arewa maso gabashin kasar.
Sanarwar ta ce za ta gudanar da bincike ta hanyar tambayar katin dan kasa a jihohin Adamawa da Borno da Yobe, kuma duk wanda aka samu ba shi da wannan takarda, to za a gudanar da bincike kansa domin gano ko ya nada alaka da kungiyar ta boko haram.

A makon da ya gabata , Sojojin Najeriya suka rufe wata cibiyar agaji tare da dakatar da harkokin da take gudanarwa na jin kai, bayan da suka zargeta da taimakawa kungiyar boko haram da kayan abinci gami da magani.