Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Tsawaita Dokar ta Baci A Nijar...Yankunan dake fama da matsalar tsaro
Gwamnatin ta Nijar ta sanar da tsawaita dokar ta baci da watanni uku a jihar Diffa dake kudu maso gabashin kasar.

Gwamnatin ta ce ta dau wannan matakin ne saboda matsalar tsaro mai nasaba da kungiyar Boko haram da yankin ke fama da ita, a don haka ta tsawaita dokar data fara aiki daga ranar 18 ga watan satumban nan.

Haka kuma gwamnatin ta tsawaita irin wannan dokar da watanni uku a jihar Tillabery, a lardunan da suka hada da Ouallam, Ayérou, Bankilaré, Abala, da Banibangou, da Say, da Torodi da kuma Téra), sai kuma a jihar Tahoua a lardunan da suka hada da Tassara da Tillia), wadanda gwamnatin ta ce har yanzu an kasa samun sukuini saboda matsaloli masu nasaba da gungun kungiyoyi ‘yan ta’adda a iyaka da kasar Mali.

Gwamnatin ta NIjar ta sanar da hakan ne a yayin taron majalisar ministocinta na jiya Juma’a.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu