Dubun dubatan Alummar kasar Zimbabwe da suka hada da wakilai da jakadun kasashen duniya ne cikin Jimami suka halarci jana’izar tsohon shugaban kasar Zimbabwe Marigayi Robeort Mugabeda aka gudanar a kasar , a babban filin wasan kwallon kafa dake birnin Harare.

Indaka sassauto da tutar kasar Kasa kasa, kana sojojin sun yi faretin girmamawa ga gawar marigayi.

Da yake bayani a wajen Janaizar shugaban kasar ta Zimbabawe Emerson Mnangwagwa ya bayyana marigayin a matsayi gwarzon dan kishin kasa, kuma rasuwarsa baban rashin ne ga kasar Zimbabwe da ma nahiyar Afrika baki daya, kuma yana fatan alummar kasar za su yi koyi da kyawawan halayensa wajen kara kaimi domin ci yar da kasar gaba.

Shuwagabannin kasashen Kenya, Afrika ta kudu Equatorial Guinea da wakilan kasashen Cuba, Rasha, da sauran kasashe na duniya sun gudanar da jawabai a wajen janaizar, ind dukkansu suka ambanci irin sadaukarwa da gudunmawar da tsohon shugaban ya bayar wajen gina kasar, da neman yanci kasashen Afrika,.

A ranar 6 ga watan Satumba da muke ciki ne shugaba Mugabe ya rasu a wani asibiti a Kasar Singapor yana dan shekaru 95 a duniya.