Daliban jami’o’i da kuma na makarantun gaba da Piramare a birnin tarayyar Najeriya, Abuja, sun yi kira ga gwamnati da ta dauki mataki domin dakile dumamare duniya. 

Daliban sun yi wannan kiran ne dai a yayin wani taro da wani shiri na samar da abinci da kuma kare yanayin duniya ( GIFSEP) ya gabatarwa kubgiyar dalibai da matasa
Shugaban kungiyar dalibai masu karatun ilimin kimiyyar kasa, a jami’ar Abuja, Malam Aliyu Sadiq, ya ce; taron ya bai wa dalibai, musamman matasa wata dama domin gabatar da mafita akan matsalar dumamar yanayin duniya.

Sadiq ya kara da cewa; Muna yin kira ga gwamnatin da ta sake rubanya kokarin da take yi domin fuskantar matsalar sauyin yanayi. 

A cikin kwanakin bayan nan dai, matasa da samari a kasashe daban-daban na duniya sun gudanar da gangami domin fadakar da al’ummar matsalar da ake fuskanta dangane da sauyin yanayi