Fiye da mutane 1000 ne rikicin kabilanci ya raba da muhallinsu a cikin shekara guda a kasar Habasha.

Babban mai shigar da kara na kasar ta Habasha y ace; fadace-fadace da ake yi a tsakanin kabilu ya ci rayukan mutane 1,200 a cikin watanni 12, sannan kuma ya tarwatsa wasu mutanen da adadinsu ya kai miliyan 1.2.

Tushen rikici a tsakanin kabilun shi ne kokari samun iko da kasar noma da sauran abubuwa masu amfani da su ka hada da son shimfida iko.Adadin mutanen kasar ta Habasha mai kabilu da yawa ya kai miliyan 100.

Tun daga shekarar 1991 ne kabilar Tigrayans ta mamaye harkokin iko a kasar, duk da cewa adadinta bai wuce 6% na al’ummar kasar ba.

Shugaban kasar Habasha Abiy Ahmad yana kokarin ganin an dinke barakar da take a tsakanin kabilun kasar ta hanyar yin sulhuatsakaninsu da kuma basu damar damawa da su a sha’anin mulkin kasar.