Da yammacin yau 1-9-2019/2-1-1441H
Yan Uwa Musulmai almajiran Sheikh Zakzaky na kaduna sun gudanar da zaman makokin Imam Hussain (As)

Bayan gabatar da wakokin juyayi dakan kirji, sai a wakilin yan uwa na da'irar kaduna, Malam Aliyu Tirmiz ya gabatar da jawabi. Malam ya fara jawabin sa ne da ta'aziya ga manzon Allah, da Ahlul-Bayt (As), da ma dukkanin al'ummar musulmai.

Sannan ya ciga da cewa zai zama abin takaici al'umma su kasa sanin watanni musulunci, da kuma abin da ya faru a tarihim musulunci, Lallai wannan abin takaici ne, yace: zaka ga yaro a boko tin ya na primary 1 ko 2 ya haddace watannin boka, amma babban mutum sai Kaga bai san watan musulunci ba, wannan yana daga tsarin bature ya sanya albashi a karshen wantan boko, hutun aiki ma haka, da dai sauran abubuwa.

A dayan bangaren kuma Malam ya ka ra da cewa: sadaukarwar da Imam Hussain (AS) babban lamari ne wanda tarihi ba zai manta da shi ba, domin kuwa abin da ya yi shi ne sirrin wanzuwar addinin muslunci bisa hakikanin koyarwar manzon Allah.

To kardai mu cika ku da surutu ga mai bukatar Audio ya shiga link din mu na Telegram
https://t.me/KadunaPress dan saura ra.

Daga karshe an sake gabatar da wakoki na juyiyi sannan a kayi addu'a a tashi.