A yau Lahadi 22 ga watan September 2019, daidai da 23 ga muharram 1441,
Aka gudanar Jana'izar Shahid Ma'aruf Umar Malumfashi.

Shahid Ma'aruf ya yayi shahada ne sakamakon harbin da Jami'an Tsaron Yan sandan Najeriya suka yi masa a ranar Talata 10 ga muharram 1441 a garin Malumfashi. 

Bayan An kai asibitin federal medical Centre Katsina, wanda daga baya aka fahimci tetanus ta shiga kafar tasa, kuma ita ce ta yi sanadiyyar shahadar sa a jiya Asabar 21-9-2019.

Sheikh Rabi'u Funtua ya jagoranci yi masa sallar.

Shi dai wannan  Shahidi Ma'aruf Umar Malumfashi, cikekken dan garin Malumfashi ne, a jihar Katsina.
Muna Allah ya ta shi tare da shahidan Karbala.

KNPRSCD 07
Kaduna Press
22-9-2019