Da safiyar yau laraba 11/9/2019, da misalin karfe biyu 8:30am, a ka gudanar da Jana'izar Shahidai Biyu Shaheed Ibraheem Abdullahi, da Shaheed Mustafa Nasiru Zikiri kaduna. 


Idan mai karatu bai manta ba, shidai wadan nan nan Shaheedai sun yi shahada ne sakamakon harin ta'addancin da jami'an tsaron yan sandan najeriya suka kawo, a kan masu muzaharar Ashura, a jiya talata 10-9-2019 a junction din bakin ruwa  dake kan titin bypass daura Hayin Rigasa a garin kaduna.


Anyi masa sallah ne a nan cikin Hayi daga bisani sai a ka kai su makwan cin su, inda a ka bizne su ana. aka gabatar a addu'o'i da dan jawbai, a kan masu afkar da shahada, da tinatarwa a kan halin da jagora ya ke ciki da kuma yadda muka samu kan mu, da nauyin da ke karu a kan mu game da iyalan Shuhada, sannan akayi addu'a a ka watse. 

Muna fatan Allah ya amshi Shahadar su tare da duk Shahidan mu, ya kuma Kwato mana jagoran mu daga hannun azzalumai. 

KNPRSCD 07
Kaduna Press