Babban bankin Najeriya CBN ya bada sanarwan cewa ya kara yawan kudaden khidima a kan asusun daddaikun mutane da kamfani daga ya Talata.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto daracta mai kula das ashen tsare-tsaren khidimomin bankin Mr Sam Okojere yana cewa daga yanzu bankin zai rika daukar kasha 3% na kudaden da fitar da su daga bankin, sannan kasha 2% na wadanda aka zuba cikin asusun daddaikun mutane idan kudaden sun fi Naira 500,000.

Sanarwan ta kara da cewa kamfanoni kuma zasu rika biyan kudaden khidima na kashi 5% na fitar da kudade sannan kasha 3% na kudaden da aka zuba a asusun kamfanin idan kudaden sun finaira miliyon 3.

Sanarwan ta kara da cewa babban bankin tad au wannan matakin ne don kara kyautata tsarinta tattalin arzikin da babu takardun kudade. Har’ila yau da kuma samarwa gwamnatin kudaden shiga.