Daga Nasir Isa Ali
Kaduna Press

Manjo janar Yahya Rahim Safavi,shine babban mai kula da tsaron jagoran juyin juya halin musulinci a Iran,ya yi gargadin cewa "idan Amurka ta yi yunkurin kai wani hari a kan Iran,to Jamhuriyar Musulunci za ta mayar da martani daga inda ita Amurka ta faro nata domin dakile yunkurin nata,kuma tabbas zata yi nadama kuma zaman ta a tekun Bahar Rum zuwa tekun Indiya ya zo karshe.

Manjo janar Rahim Safavi ya ce "cikin hikimar Allah da taimakonsa mun samu sojoji masu wani irin jaruntaka da juriyar wajen sadaukarwa,sannan al'ummar Iran karan kanta al'umma ce dake da komajin sadaukarwa wajen kare addininsu da kasarsu ,wanda kuma sun yi sadaukarwar a baya wacce ba za'a iya mantawa da ita ba, Al'ummar Iran ta zama mai karfi a yankin Yammacin Asiya, "saboda dogaronta ga Allah da kuma daukar matakin Sadaukarwa in ji Manjo Janar Rahim Safavi, yayin da yake gabayar da jawabi (Pre-Khutuba) ga dubban taron masallata a birnin Tehran ranar Juma'a 20/9/2019 - Ya kara da cewa "Idan Amurkawa suna tunanin kulla mana wani makirci,to za mu tabbatar mun mayar musu da martani mai gauni dai dai da makircin nasu, kuma sai mun sa Tekun Bahar Rum da Bahar Maliya zuwa Tekun Indiya duk sun gagare su zama inji Janar Rahim Safavi. Babban jami'in tsaro ga Jagoran addinin ya kara yin wani gargadin ga wasu kasashen yankin da cewa, "Duk wani yunkuri na kawo wa Iran hari daga wasu kasashen yankin Gulfnko Asiya zai sa yakin gabaki daya ya fada cikin rikici, kuma kowa sai ya dandana kudarsa in ji babban jami'in sojan. Ya kara da cewa Amurkawa sun sani sarai cewa Iran kasa ce mai karfi da sukkanin ma'anar karfi, kuma tana da tsayayen jagorara sannan ga jaruman sojoji da kuma dakaru masuƙkarfi da kumajin sadaukarwa. - 

"Manufarmu kamar yadda muka sha fada, ita ce samar da dawwamammen zaman lafiya da tsaro ga yankin namu tare da neman janyewar duk wasu sojojin kasashen waje daga yankunan namu baki daya.. Kuma Iran ta sha fadar cewar bata da niyar mamaye kowacce kasa ko fadada kasarta zuwa wata kasar,kuma tana mutunta kowa.

Kuma bata shiga wata kasar domin aikin tsaro face sai da izinin ita kasar. Wannan jawabin na Janar Safawi ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashin tashina tsakanin Iran da Amurka tun bayan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta harbo wani jirgin leken asiri Amurka (Global Hawk) a yankin ruwanta na Hourmozgan. Sannan sai kuma hare-haren baya-bayan nan wanda sojojin Yemen suka kai kan matatun mai na masarautar Saudiyya 'Aramco Oil. -

Rundunar (IRGC) ta sanar a ranar 20 ga watan Yuni cewa, dakarunta sun harbo wani jirgin leken asirin Amurka da ya keta mata dayaucin sararin samaniyarta.Ta ce ta harbo shi ne a yankin Kooh-e-Mobarak a cikin. lardin kudancin kasar na Hormozgan da wani makami mai linzami mai suna "Khordad-3rd". -

Bayan da rundunar Ansarullah suka kai wa Saudiya munanan hare hare,Saudiyar da Amurka sun yi wuf suka zargi Iran da kai harin, abin da masana ke kallo da cewar 'Amurka tana neman wasu dalilai ne na kai wa Iran din harin soja. In ba haka ba,ga wanda ya fito yayi ikirarin cewar shine ya kai harin to ai zance ya kare,amma menene kuma na tuhumar wata kasar ta daban?? - Nasir Isa Ali