An ga jami’an tsaro a cikin muhimman wurare na babban birnin kasar alkahira domin hana mutane sake haduwa saboda su yi Zanga-zanga.

A ranar juma’ar da ta gabata ne dai daruruwan mutane su ka taro a kusa da dandalin Tahrir suna yin kira ga shugaban kasar Abdulfattah al-sisi da ya yi murabus
Jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu Zanga-zangar ta shekaran jiya juma’a.

Zanga-zangar dai ta zo ne a matsayin amsa kira wani fitaccen dan kasuwar kasar Muhammad Ali ga mutanen kasar da su fito domin kifar fa gwamnatin al-Sisi.
Abdufattah al-sisy ya hau karagar mulkin kasar ta Masar ne bayan kifar da gwamantin Muhammadu Mursi a 2013.
Ana daukar Zanga-zangar ta shekaran jiya a matsayin wani babban kalubale a gaban shugaba Adbulfattah al-Sisiy