Kotun koli a kasar Burtaniya ta bada umurnin a sake bude majalisar dokokin kasar, bayan da firai ministan kasar Boris Johnson ya bukaci sarauniya Elizabeth II ta amince da rufe ta a cikin yan kwanakin da suka gabata, sannan dab da makonnin kadan kasar ta fice daga tarayyar Turai.
Alkalan kotun kolin guda 11 sun gamu a kan sake bude majalisar a wani hukuncin da suka yanke a yau Talata, sun kuma bada umurnin a bude majalisar daga gobe Laraba.

Boris Johson dai bai da goyon bayan mafi yawan yan majalisar dokokin kasar na Britaniya, sannan da alamun zai fuskanci matsaloli masu yawa idan majalisar to kuma aiki daga gobe Laraba.

Har’ila yau a wani larabin tarayyar Turai ta bada sanarwan cewa sabuwar bukatar sake tattauna batun ficewar Burtaniya daga tarayyar wacce gwamnatin Johnson ta gabatar ba abu ne mai yiyuwa ba.

Michel Barnier, mai tattaunawa a matsayin tarayyar Turai dangane da ficewar Burtaniya daga tarayyar ta Turai, ya fadawa yan jaridu cewa a sabuwar bukatar sake tattaunawar da Burtaniyar ta gabata akwai batun yin watsi da ficewar yankin Island ta arewa daga ikon Burtaniya idan har ta fice daga tarayyar a ranar 31 ga watan Augusta mai zuwa.

Michel Barnier, ya ce tarayyar Turai ba zata taba sauya matsayinta na wanzuwar yankin Island a cikin tarayyar Turai ba.