Babbar kungiyar ‘yan sanda a Burkina faso, ta yi barazanar janye jami’anta daga yankunan dake fama da barazanar ta’addanci, idan har ba’a tanadar masu da ingatatun kayan aiki ba.

Kungiyar ta ce zata janye daga cibiyoyi ashirin na yaki da ta’addanci a yankuna shida na kasar saboda rashin isasun kayan aiki, kamar yadda ake baiwa sauren takwarorinsu.

‘yan sanda dai na bukatar ‘yan siyasa kasar dasu dauki batun tsaro da mahimmanci, tare da kira ga al’ummar kasar akan su basu hadin kai wajen yakar ta’addanci.
Ko a ranar 12 ga watan Satumban nan, ‘yan sanda dama ne suka janye daga yankin Djibo dake arewacin kasar mai fama da matsalar tsaro.

Da yake maida martini kan barazanar kungiyar ‘yan sanda, kakakin gwamnatin kasar, Rémi Dandjinou, ya ce ya gamsu da wasu bukatun ‘yan sanda, saidai a cewarsa janyewar ‘yan sanda daga yankunan zai amfani ‘yan ta’addan ne.