Kakakin rundunar sojin kasar Yemen ya sanar da kaddamar da wani gagarumin farmaki mai taken “Nasrun Minallah” a kan dandazon sojojin Saudiyya da kuma ‘yan korenta a Najran.

Tashar Almasirah daga kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jiya a birnin San’a fadar mulkin kasar Yemen, Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Brigadier General Yahya Sari ya bayyana cewa, dakarun kasar sun samu nasarar kaddamar da wani gagarumin farmaki mai taken “Nasrun Minallah” a kan dandazon sojojin Saudiyya da kuma ‘yan korenta daga kasashen ketare a Najran.

Ya ce an dauki tsawon watanni ana aiwatar da shirin wannan farmaki wanda ya gudana a cikin nasara, inda ya ce sun kama dubban sojoji a matsayin fursunonin yaki wadanda suka mika kansu da makamansu, bayan da dakarun na Yemen suka rutsa da su.

Haka nan kuma Yahya Sari ya kirayi iyalan wadanda aka kame a matsayin fursunonin yaki da su kwantar da hankulansu, domin kuwa ana ba su kulawa tare da kyautatawa kamar yadda addinin muslunci ya umarta.
Wannan farmaki kan dakarun Saudiyya da ‘yan korenta da kuma sojojin hayar da ta dauka daga kasashen ketare na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan harin ramuwar gayya da dakarun na Yemen suka kaddamar kan babban kamfanin mai na kasar Saudiyya Aramco, wanda hakan ya yi sanadiyyar tsayawar mafi yawan ayyukan kamfanin a halin yanzu.

Saudiyya dai ta kwashe tsawon shekaru kusan biyar tana kaddamar da hare-hare ta sama da kasa da kuma ta ruwa a kan al’ummar kasar Yemen, lamarin da majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa ya yi sanadiyyar mutuwar dubban fararen hula, tare da jikkata wasu, da kuma haifar da asarori masu tarin yawa ga al’ummar kasar ta Yemen, da kuma jefa su cikin matsananci hali na rayuwa.