Dan takarar shugabancin kasar Tunsia da ya fi dukkanin sauran 'yan takarar samun kuri'u a zaben da aka gudanar zagaye na farko a kasar ya ce; babu batun kulla duk wata alaka da Isra'ila.

Shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, a wani bayani da ya saka a shafinsa na yanar gizo, Qais Sa'id dan takarar shugabancin kasar Tunsia da ya fi dukkanin sauran 'yan takarar samun kuri'u a zaben da aka gudanar zagaye na farko a kasar ya bayyana cewa; idan har ya lashe zabe a zagaye na biyu, ba zai kulla alaka da Isra'ila ba.

Ya ce kulla alaka da Isra'ila yana a matsayin cin amana ne ga dukaknin al'ummar kasar Tunisia, wadanda ba su amince da samuwar Isra'ila ba.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, duk wani shugaban kasar Tunisia da ya kulla alaka da Isra'ila, to ya aikata babban laifi da al'ummar Tunisia ba za su taba yafe masa ba, ko da kuwa kotun kolin kasar ta halasta masa yin haka, domin al'ummar Tunisia suna tare da 'yan uwansu ne al'ummar Falastinu.